Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wata Kungiya Ta Nuna Rahin Jin Dadin Ziyarar Da Obasanjo Ya Kai Binuwai


Olusegun Obasanjo

Ana wata; ga wata. Yayin da wasu ke yaba ziyarar da tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya kai jahar Binuwai (Benue), wasu kuma kushewa su ke yi saboda su na ganin shi ma a baya ya yi sanadin mace-macen wasu mutane.

Palay Scharancham, kakakin wata kungiya mai da'awar kare dimokradiyya ya ce tunda tsohon shugaban kasa Olushegun Obasanjo na sha'awar aza furanni kan kaburburan wadanda aka kashe a sakamakon fitintinu daban daban to suna gayyatarsa ya shiga yankin Zaki Biyam, wanda ya kunshi Taraba da Rivers da Filato, domin aza irin wadannan furannin.

Kungiyar ta nuna korafi kan ziyarar da Obasanjo ya kai Benue da aza furanni kan kaburburan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon rigimar makiyaya da manoma, inda kungiyar ke ganin maida lamuran kaburbura tamkar biki na kara haddasa kiyyaya tsakanin jama'a.

Tasiu muhammad ringim na cikin wadanda suka shirya taron, ya bayyana cewa ya kwarance wajen inganta sharri da kawo baraka tsakanin al'umma kuma duk abinda za a yi, idan bai tafi daidai dashi ba, sai ya bi hanyar da zai la'anta shi.Wani dan kabilar idoma daga Benue ya bayyana cewa ba lallai duka shanun da ake kashewa ne mallakar fulani ba, don akwai fulani tamkar leburori da ke bin shanun wasu, ya kara da cewa basu makaman yakin ake yi ba wai suna da kudin saye ne da kansu ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG