Tsohon mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden, ya samu gagarumar nasara akan abokin hamayyarsa Sanata Bernie Sanders na jihar Vermont a zaben sharar fage da aka yi na jam’iyyar Democrat a jihohi hudu.
Daga cikin jihohin har da ta Michigan da ke tsakiyar yammacin Amurka.
Wannan shi ne karo na uku da yake neman mukamin shugaban kasar cikin sama da shekara 30.
Nasarar ta kuma sa ya kara samun damar yiwuwar karawa da Shugaba Donald Trump a watan Nuwamba.
Baya ga Michigan, ya kuma lashe jihohin Mississipi da ke kudancin Amurka da kuma Idaho da ke yammaci.
Wadannan nasarori da Biden ya samu a jiya Talata, sun kuma kara sa ya zama abu mai wuya Sanders, wanda ya ayyana kansa a matsayin mai ra’ayin Democrat kuma dan gurguzu, ya wuce shi wajen samun tikitin jam’iyyar ta Democrat.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 23, 2021
Jirgin Hukumar Sama Jannatin Amurka Ya Isa Tashar Sararin Sama
-
Fabrairu 22, 2021
COVID-19 :Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kusa Rabin Miliyan A Amurka
-
Fabrairu 20, 2021
Amurka Ta sake Komawa Cikin Yarjejeniyar Sauyin Yanayi A Hukumance
-
Fabrairu 17, 2021
Texas-Dussar Kankara Ta Haifar Da Dauke Wuta A Gabashin Amurka