Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bikin Ranar Malamai Bai Yi Armashi Ba a Jihar Adamawa


 Irin yanayin da yara ke karatu ke nan a makarantun gwamnatin jihar Adamawa
Irin yanayin da yara ke karatu ke nan a makarantun gwamnatin jihar Adamawa

Kodayake an shirya bikin tunawa da ranar malamai ta Majalisar Dinkin Duniya a jihar Adamawa, malan jihar basu ji dadin ranar ba saboda har yanzu gwamnati bata biyasu kudadensu ba kana dakunan karatun yara wasunsu kamar dakunan awakai suke

Bikin wannan shekara na “Ranar Malamai Ta Duniya” da Asusun Kula Da Yara na Majalisar Dinkin Duniya yakan shirya a kowace ranar biyar ga watan Oktoba don yin juyayin halin da harkar ilimi take ciki da aka gudanar a jihar Adamawa bai yi armashi ba saboda abinda da malaman suka kira alkawurran romon baka da gwamnatin ke yi amma bata cikawa a duk zagayowar wannan rana.

Wasu malamai da suka halarci bukin tunawa da ranar wadda aka kaddamar a Dandalin Mahmud Ribadu da ke Yola, fadar jihar, sun bayyana rashin fitowar malamai musamman na matakin firamare da rashin tasirin sa a rayuwarsu a kan matsalolin da suke fuskanta, da suka hada da bashin albashin wattani uku da suke bin gwamnati, da kudin alawus na hutu na shekaru biyar, ga shi kuma rabon da a yi wa malamai karin girma tun shekarar 2002.

Mataimakin gwamnan jihar, Injiniya Marthins Nasiru Babale ya shaidawa taron malaman cewa gwamnati na nazarin yadda zata magance matsalolinsu, kana ya yi anfani da ranar wajen kira akan kanfanoni, masana’antu, kungiyoyi da mutane masu hannu da shuni su taimakawa gwamnati wajen farfado da harkar ilimi.

Sai dai kalaman, ga alamu, ba su yi wa malaman dadi ba, da yake suna tsammanin cewa gwamnati zata shata jaddawalin magance matsalolin nasu.

Da yake wa manema labarai bayaniakan sakon “Ranar Malamai Ta Duniya” na bana mai taken ‘biyan hakkokin malamai da samar da yancin karantarwa cikin walwal da tsaro, shugaban Kungiyar Malamai Ta Najeriya reshen jihar Adamawa, Komrad Rodney Nathan ya ce fatar kungiyar ce ta ga ranar da gwamnati zata cika alkawurran da ta sha dauka babu cikawa.

Asusun Kulawa Da Yara na UNESCO ya kudurta

tabbatar da bai wa harkar malanta fifiko karkashin shirin tabbatar da dorewar Muradan Karni kan nan da shekara ta 2030.

Saurari karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG