Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biritaniya Zata Mayarda 'Yan Najeriya Fursinoni Zuwa Kasarsu


Shugaban Najeriya da ya yarda da yarjejeniyar

Gwamnatin Biritaniya na shirin mayarda da fursinoni 'yan kasashen waje zuwa kasashensu cikinsu har da Najeriya

Sabili da dumbin kudaden da take kashewa kan fursinoni gwamnatin Biritaniya na shirin mayarda 'yan kasashen waje dake gidajen kaso a kasar zuwa kasashensu na haihuwa. Akwai 'yan asalin kasar Najeriya ne da dama.

A watan Afirelun bara wata kotu a birnin London ta yanke wa tsohon gwamnan jihar Neja Delta ta Najeriya James Ibori hukuncin daurin shekara goma sha uku a gidan kaso sabili da ta sameshi da laifin satar kudin jihar kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 77 ko kuma nera miliyan dubu goma sha uku. Ministan Kurkuku na Biritanya ya ce burinsa shi ne mayarda fursinoni 'yan kasashen waje zuwa kasashensu kamar 'yan Najeriya domin su karasa hukuncin da aka yi masu.

Gwamnatin Biritaniya ta dade tana tattaunawa da gwamnatin Najeriya batun mayarda fursinoni 'yan asalin Najeriya zuwa kasar su cigaba da hukuncin dauri da aka yi masu. Gwamnatin Biritaniya ta kiyasta cewa daga kowane fursinoni takwas biyu 'yan kasashen waje ne. Gwamantin Biritaniya tana kokarin rage makudan kudin da take kashewa kan fursinoni. Ministan ya ce gwamnatin na kashe kusan fam dubu arba'in a kan fursina daya kowace shekara wato kimanin nera miliyan goma sha daya ke nan.

A yarjejeniyar da suka yi gwamnatin Biritaniya zata ba Najeriya taimakon kudi fam miliyan daya ko nera miliyan dari biyu da saba'in domin ta gyara wasu gidajen kaso kamar kirikiri dake Legas. Kawo yanzu akwai 'yan Najeriya 532 dake gidan kaso a Biritaniya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

LABARI: “Akwai cigaban wannan labari, da wasu labaran masu dumi-dumi, da hotuna, da bidiyo, da cikakkun shirye-shiryen mu duk a shafinmu na www.voahausa.com.”

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG