Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birnin Houston zai kara samun ambaliyar ruwa


Ambaliyar ruwan da Houston ke fama dashi yanzu

A yayin da dubban mutane a unguwannin da ke Houston ta jihar Texas a nan Amurka ke fama da yadda zasu shawo kan asarar da ambaliyar ruwa a ranar Litinin da ta wuce ta haddasa masu, sai kuma ga rahoton wata guguwar ruwa na tafe daga tekun Mexico da zai kara dagulewa mutanen garin sha’ani.

Kafaffun koguna da gulbi na daga cikin abinda suke dada ta’azzar wannan ambaliya, wanda har mutane akalla 8 sun mutu daga guguwar mai hade da ruwan sama da ta fara a yammacin Lahadi zuwa ranar Litinin din data wuce.

Gwamnan jihar Texas Greg Abbott, tuni ya sa dokar karta kwana ta annoba akan dukkan kananan hukumomi 9 da ruwa ya shanye. Jihar Texas dai itace ta 4 mafi girma a nan Amurka ta yi tsit da hada-hadar kasuwanci a yayin da wannan masifa ke ci gaba.

Masu ayyukan ceto sun ceci akalla mutane 1,200 da wannan ambaliya ta bari suna walagigi. Fiye dai da gidaje 1000 ne suka lalace tare da daukewar wutar lantarki a wurare da dama. Abin ya fi shafar yawanci wadanda ke zaune a gidajen kasan benaye.

Irin barnar da ambaliyar ruwa ya riga ya yi a Houston
Irin barnar da ambaliyar ruwa ya riga ya yi a Houston

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG