Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Na Shirin Fidda Kamfanin Huawei a Shirin Samar Da Fasahar 5G


Gwamnatin Birtaniya na shirin fidda Huawei, mashahurin kamfanin nan na sadarwar China a shirin samar da sabuwar ingantantacciyar fasahar sadarwa ta 5G, abinda wasu ke ganin Birtaniyar ta yi amai ta lashe kan batun da ake hasashen zai sake raunana dangantakar London da Beijing, sannan a gefe guda kuma ake ganin zai faranta wa hukumomin Washington rai, kamar yadda kafofin yada labaran Birtaniya suka ruwaito.

Wannan babban sauyi da Birtaniya ta yi, ya biyo bayan wani sabon nazari da hukumar tsaron rumbun bayanan kasar ta NCSC ta yi, kan yiwuwar kamfanin na China ya rika satar bayanan kasar, kamar yadda jaridar Telegraph da ake wallafawa a Birtaniya ta ruwaito a ranar Lahadi.

Tuni dai hukumomin Birtaniyar suka tabbatarwa Muryar Amurka gaskiyar rahoton na jaridar ta Telegraph.

A baya, hukumar ta NCSC wacce ke karkashin cibiyar tattara bayanan sirrin Birtaniya ta GCHQ, ta ce ta yiwu a iya shawo kan barazanar tsaron da kamfanin na Huawei ya janyo a kuma rage karfinta, lamarin da cibiyoyin leken asirin Amurka ba su lamunta da shi ba.

Amma hukumar ta NCSC ta ce, sabbin ka’idojin da Amurka ta saka wa kamfanin Huawei ya sa Birtaniya ta sauya matsayarta.

Ranar Lahadi 5 ga watan Yuli kamfanin ya fitar da wata sanarwa, yana mai cewa a shirye ya ke ya hau teburin tattaunawa da gwamnatin Birtaniya, ya kuma zargi Amurka da yunkurin ganin kamfanoninta sun samu kwantaragin gudanar da aikin.

Huawei ya kuma ce ikirarin da ake yi cewa zai saci bayanai idan aka ba shi damar samar da sabuwar hanyar sadarwa ta 5G duk shaci-fadi-ne.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG