Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Birtaniya Ta Musanta Zargin Neman Canza Gwamnatin Sudan ta Kudu


Shugaban 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar
Shugaban 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar

Sudan Ta Kudu ta zargi wasu kasashen yammacin turai da suka hada da Amurka da shirya wata makarkashiyar hambarar da gwamnatin kasar tare da hadin gwuiwar 'yan adawan kasar

A halin yanzu kuma...wani kakakin kungiyar dakarun S-P-L-A ta Sudan ta Kudu yace wakilan gwamnatocin kasashen Amurka, Biritaniya da Norway sunyi wani taron asiri da kusoshin ‘yan adawa na Sudan ta Kudu masu biyayya ga tsohon mataimakin shugaban shugaban kasar, Riek Machar a birnin Nairobin Kenya a farkon watan nan, kuma yace ba abinda suka tattauna illa yadda za’a tumbuke gwamnatin Sudan ta Kudu, a kafa wata sabuwa.

A jiya Alhamis ne mataimakin kakakin rundunar sojan kasar, Col. Santo Dominic Chol yake wannan zargi a ganawar da yayi da manema labarai a birnin Juba.

Tuni dai gwamnatin Biritaniya ta musanta zargin, inda tace wannan zargin da aka yi a cikin wata jarida mai suna “East African” soki-burutsu ne kawai da bai nuna manufar gwamnatin ta Biritaniya ba.

Har yanzu gwamnatin Amurka dai bata riga ta maido murtani akan wannan rahoton ba.

XS
SM
MD
LG