Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fitaccen limamin Majami'ar Sacred Heart, karkashin darikar Katolika a garin Shandam, Bishop James Daman ya riga mu gidan gaskiya.

An haifi James Daman a garin Kwa dake Najeriya, a shekara ta 1956.

Ran 14 ga watan Fabrairu na 1982 ne aka nada Mr. Daman domin zama Fada a Majami'ar St. Augustine a Jihar Taraba, sannan an zabe shi a matsayin Bishop na garin Jalingo ranar 5 ga watan December shekara ta 2000, sannan aka nada shi ran 24 ga watan Fabrairun 2001.

Marigayi Bishop Daman ya samu daman zama Bishop na majami'ar Sacred Heart dake garin Shendam a jihar Filato ran 2 ga watan Yuni a shekara ta 2007.

Mr. Daman ya rasu ran 12 ga watan Junairu na 2015, kuma an binne shi ran 29 ga watan Junairu na 2015 a garin Shendam.

Bishop James Daman
Bishop James Daman

Bishop James Daman ya share shekaru 33 yana aikin Fada, sannan ya share shekaru 13 da watanni goma yana aikin Bishop.

XS
SM
MD
LG