Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram:An Kashe Kimanin Ma’aikatan Kananan Hukumomi Dubu Biyu


'Yan gudun hijira baza su yizabe ba, Maris 20, 2015.

Yanzu haka alkalumma na nuni da cewa fiye da ma’aikatan kananan hukumomi dubu biyu ne rikicin Boko Haram yayi sanadiyar mutuwarsu a jihohin Adamawa,Borno da kuma jihar Yobe, Yayin da kawo yanzu wadansu ma’aikatan da suka yi gudun hijira basu komo ba,lamarin dake kara tada hankalin kungiyar ma’akatan kananan hukumomin Najeriya NULGE.

Baya dai ga asarar rayuka ,haka nan ,yan Boko Haram sun lalata makarantu,da kuma ofisoshin gwamnati baya kuma ga wadanda suka kona,lamarin da yanzu haka ya tsaida harkokin gwamnati a wadansu kananan hukumomin da suka yi ta’adi.

Kwamred Emannuel Fashi shugaban kaungiyar na jihar Adamawa wanda kuma shine shugaban yada labaran kungiyar a Najeriya, yace kawo yanzu sama da ma’aikata dubu biyu ne suka rasa rayukansu ta dalilin hare haren kungiyar Boko Haram, baya ga wadanda suka bace, yace suna kokari domin tallafawa wadanda abin ya shafa.

Yanzu yace da lamura suka fara daidaita, zasu gudanar da bincike domin tantance wadanda aka kashe da wadanda suka kauracewa matsugunansu ala tilas. Kasancewa.

Duk da yake shugabannin kungiyar sun ikirarin cewa suna iyakar iyawa domin ganin sun kula da membobinsu, wadansu membobin sun bayyana cewa, shugabannin basu kula da lafiyarsu ba sabili da haka suke kokarin saukesu su nada wadanda suka ce zasu kula da jin dadinsu.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu Ibrahim Abdul’Aziz ya aiko mana daga Yola, Najeriya.

Rikicin NULGE-3:00
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG