Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram - Fuskokin Ta'addanci


BOKO HARAM: Fuskokin Ta'addanci

A kalla ko karanta rahotanni na musamman na VOA Hausa dangane da faya-fayen bidiyon sirri na Boko Haram.

Karin bayani akan Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci >

An fito da wani karamin yaro a fili ana masa bulala.Masu kallo sun taru suna kabbara yayin da ‘yan boko haram ke harbin mutane a kirji da kuma a kai. Abun ko a jikinsu duk da irin ihun tuba da kin amsa laifin da suke yi.

Wannan rohoton da zai biyo zai nuna ‘yan kungiyar boko haram a fili daga wasu bidiyoyinsu da suka dauka da kansu. Muryar Amurka ta samu wadannan bidiyoyin da ka iya fusata mai kallo.

A wani kauye dake arewacin Najeriya mai suna Kumshe, Kungiyar Boko Haram ta zartar da hukunci kan mutane bisa mummunar fassarar da suka yi wa shari’ar musulunci.Suna yanke hukunci mai tsanani ga wadanda suka kama da laifuka kamar saka tufafi irin na turawan yamma ko don yin karatun boko da sauransu. Ana yankewa wadanda aka zarga da sayar da kayen maye hukuncin bulala ko kisa kamar yadda za’a gani a bidiyoyin.

Karin bayani akan Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci >

XS
SM
MD
LG