Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram: Mayaka Sun Sake Salon Kai Hari


‘Yan sanda na tattara tarkace a wajenda bom ya tashi, a garin Nyanya dake Abuja.

Kungiyar Boko Haram ta sake salon kai hare hare, tare da yin shigar 'yan banga domin badda kama da nufin yaudarar al'umma su kai hare hare.

Rahotanni daga jihar Adamawa,arewa maso gabashin Najeriya na cewa yanzu haka sojojin Najeriya na can na fafatawa da mayakan Boko Haram a arewacin jihar,a yankin Madagali.Wannan kuma na zuwa ne yayin da yan bindigan ke sauya salon a shigan kayaki irin na banga,wanda har suka yiwa sojoji kofar rago.

Wakilinmu Ibrahim Abdul’aziz ya ruwaito cewa, ‘yan bindigan sun kashe wadansu sojoji suka kuma yi awon gaba da wani soja. Wani mazaunin garin ya shaidawa wakilin namu cewa, I zuwa lokacin hada rahoton ana musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan bindiga a Kishinga kuma kawo yanzu ba a san adadin wadanda aka kashe ba.

A cikin hirarsu da wakilin namu, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Madagali/ Michika Adamu Kabali ya bayyana halin da ake ciki a jihar.

Ga cikakken rahoton

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG