Accessibility links

Kungiyar Boko Haram Ta Ayyana Tsagaita Wuta.

  • Aliyu Imam

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.
Jiya litinin a Maiduguri, wani mutum wanda yake ikirarin shi kwamanda ne a kungiyar mayakan sakai da aka fi sani da Boko Haram, ya ayyana shirin tsagaita wuta na kashin kai. Babu tabbas ko kwamandan Sheikh Abu Mohammed Ibn Abdulazeez, yana magana ne a madadin dukkan kungiyar baki daya, duk da haka jami’an Najeriya suka ce zasu yi nazari kan sharuddan da kungiyar ta gindaya.
Hotunan vidiyo daga tashar talabijin ta NTA da aka dauka a bara a maidugri. Babu tabbas kan hali da mutanen nan da suke kwance suke ciki.
Hotunan vidiyo daga tashar talabijin ta NTA da aka dauka a bara a maidugri. Babu tabbas kan hali da mutanen nan da suke kwance suke ciki.

Wannan ne karo na farko da wani mutum ya bayyana gaban ‘yan jarida yana ikirarin cewa shi dan kungiyar Boko Haram ne. Abunda aka saba gani daga 'yan kungiyar shine su kira da woyoyin da aka boye lambobinsu, ko su aike da sakon vidiyo a dandalin Youtube, ko sakon email, idan har suna da wani sako da suke so duniya ta ji.

A jawabi na minti 10 da ya gabatar, Abdulazeez yace shine na’ibin shugaban kungiyar Abubakar Sheaku, mutumin da aka hakikance shine shugaban kungiyar.

A jawabin da ya gabatar da Hausa, Abudlazeez ya yi kira ga ‘yan kungiyar su kwance damara, kuma su gayawa abokanansu cewa su ma su yi hakan, domin kada jami’an tsaro su kama wani “dauke da makamai ko su kashe su da sunan ‘yan kungiyar”.

Babu wanda ya san yawan rassan kungiyar Boko Haram, kuma ko wadanne ne daga cikinsu suke mutunta umurni daga kwamanda Abdulazeez. Idan aka duna daga take takensu, wadansu suna son su kafa tsarin shari’a tsantsa, wadansu kuma suna yaki ne da jami’an tsaron Najeriya.

Kamar yadda Abdulazeez ya fada ganin sun tsagaita wutar, gwamnatin jihar Borno, jihar da a can ne tungar tawayen, ta amince zata saki ‘yan kungiyar da ake tsare da su. Idan kuma gwamnatin ta kasa cika abunda ya kira “alkawari”, yace rashin zaman lafiyar zai dore har abada.

Kakakin gwamnan jihar Borno, Isa Gusau bai tabbatar da cewa jami’an gwamnatin jihar sun gana da Abdulazeez ko a’a ba. Duk da haka yace Gwamna kashim Shettima, ya sha nanata kiran da a gudanar da shawarwarin sulhu da kungiyar ta Boko Haram.

A cikin wani sakon text da ya aike cikin daren litinin, kakakin kungiyar tsaro ta musamman a jihar leftanar Sagir Musa, yace suna marhabin da shirin tsagaiata wutan, duk da haka yace ba zasu sassauta matakan tsaro da suka dauka ba, ya kira Abdulazeez shugaban Boko Haram. Kanal Sagir bai ce kome ba kan sharadi da kungiyar ta shimfida ba.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG