Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kai Hari a Kusa Da Maiduguri


Mataimakin Gwamnan Borno, Alhaji Usman Mamman Durkuwa

Wasu da ake kyautata zaton 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari Magumeri dake kusa da Maiduguri inda suka yi barna tare da hallaka wasu sojoji da har yanzu ba'a san adadinsu ba.

Mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Usman Mamman Durkuwa wanda ya ziyarci Magumeri inda 'yan Boko Haram suka kai hari jiya da yamma ya yi wa Muryar Amurka bayanin abinda ya faru ya kuma gani.

Inji mataimakin gwamnan babu talaka daya da aka kashe ko kuma gidan talaka daya da aka kone.

Sai dai sun kashe dan sandan dake tare da sojoji, sun kuma kone tankin yaki na sojoji tare da gidan radiyon da suke aika sako da tanka ta ruwa.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG