Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kai Hari Wasu Kauyukan Madagali


Wani yanki a karamar hukumar Madagali

Wasu mahara da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne sun kai wa kauyen Milbu da Kaya hari, inda suka yi garkuwa da wasu mutane uku tare da sace mota guda.

Kungiyar Boko Haram da ke ta da kayara baya a arewa maso gabashin Najeriya, ta kai wasu hare-hare a kauyan karamar hukumar Madagali da ke jihar Adamawa.

A cewar wani mazaunin daya daga cikin kauyukan, maharan sun farma kauyen Kaya ne da ke da tazarar kilomita daya daga garin Gulak, hedikwatar karamar hukumar Madagalin.

Shaidu sun ce sun kuma sace mutane uku da mota, sannan sun karyawa wata dattijuwa kafa.

Bayan da marahan suka bar kauyukan ne, jami’an tsaro suka shiga yankin da aka kai hari suna harbe-harbe a cewar wani mazaunin kauyen.

Ya zuwa yanzu dai hukumomin tsaro ba su yi karin haske game da wannan sabon hari da aka kai cikin daren jiya Alhamis ba.

Amma kuma shugaban karamar hukumar ta Madagali Hon.Yusuf Muhammad ya tabbatar da faruwan lamarin, inda har ya yabawa yan sakai na maharba da suka tarwatsa harin da aka soma kaiwa a Milbu.

Shi ma da yake karin haske, dan Majalisar wakilai da ke wakiltar yankin, Mr. Adamu Kamale, ya koka da harin da ake kai wa cikin kwanakin nan, tare da neman gwamnatin tarayya ta aika sojoji zuwa yankin kasancewar ba su da nisa da dajin Sambisa da ya kasance tungar mayakan na Boko Haram.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00

Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG