Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kashe Mutane Biyar a Nijar


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.
Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.

Kungiyar Boko Haram da ta samo asali daga Najeriya ta kai wani hari a yankin a garin Koukwandou da ke jihar Diffa, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun shiga yankin ne daga Najeriya inda suka kai harin tun a ranar Talatar da ta gabata da misalin karfe tara na dare.

Rahotanni sun ce maharan har ila yau sun yi awon gaba da motoci biyu sun kuma kona wata motar sannan sun kaiwa wasu garuruwa hare-hare da ke kusa da yankin Boso.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa maharan sun kwashi kayayyaki da dama a shagunan jama’a baya ga kone-kone da suka yi.

Bayanai na cewa dukannin wadanda suka mutu a hare-haren fararen hula ne kuma babu dakarun kasar ko daya.

Mataimakin gwamnan jihar ta Diffa Lamido Moumouni, ya tabbatar da aukuwar hare-haren inda ya ce gwamnati na kokari ta ga ta samar da cikakken tsaro a yankunan.

A farkon makon nan ne gwamnatin kasar ta Nijar ta baiwa mutanen yankin Tafkin Chadi da su fice daga wuraren, a wani shiri da hukumomi ke yi na kaddamar da hare-hare akan ‘yan kungiyar ta Boko Haram.

Ga karin bayani a hirar wakilinmu da Abdoulaziz Adili:

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:29 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG