Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram ta Kawo Cikas ga Samarda Wutar Lantarki


Harin kunar bakin wake

Hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke yawan kaiwa a jihohin arewa maso gabas sun jawo cikas ga samarda wutar lantarki sun kuma durkusar da harkokin kasuwanci.

Hare haren sun tilastawa kamfanin samarda wutar lantarki na YEDC dake kula da jihohin Adamawa, Borno da Yobe da kuma Taraba rufe ofisoshinsa ban da asarar dimbin kayan da kamfanin yayi.

Lamarin ya sa jihohin sun samu matsalar samun wutar lantarki. Alhaji Ahmed Hassan Ardo jami'in hulda da jama'a na kamfanin yace yanzu haka kamfanin na cikin wani mawuyacin hali na rashin kudaden shiga. Duk ofisoshinsu dake Borno sun rufe saidai Biu da Maiduguri. Da sukan samu nera miliyan dari da ashirin daga jama'a amma yanzu da kyar suke samun miliyan biyar zuwa shida.

A Yobe duk da wai basu rufe ofisoshinsu ba amma akwai wasu wurare da ba zasu iya zuwa ba kamar su Gujuba da Buni Yadi da sauran wuraren a Yobe dake hannun 'yan Boko Haram. Bamabaman da aka jefa a Damaturu da Potiskum sun shafi ayyukan kamfanin. Da kyar kamfanin ke samun kudin yin aiki.

Hare-haren Boko Haram sun kuma durkusar da harkokin kasuwanci a jihohin. Rufe wasu iyakokin kasar da Kamaru shi ma ya dakatar da hadahadar kasuwanci da aka saba yi a wuraren.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG