Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BOKO HARAM: 'Yan Kunar Bakin Wake Mata Hudu Sun Tarwatsa Kansu


Wadannan mata. 'yan uwan wani mutun ne da harin kunar bakin wake ya kashe, a harin da aka kai jami'ar Bayero.

Hukumomi sunce wadansu ‘yan kunar bakin wake mata hudu sun tarwatsa kansu kusa da garin Maiduguri dake arewa maso gabashin najeriya yau asabar,bayanda jami’an tsaro suka yi kokarin yi masu bincike.

Hukumomin Najeriya sun ce an kashe mace ta biyar, yayinda wadansu goma kuma suka ji rauni sakamakon tarwatsewar nakiya, lamarin da ya kasance na baya bayan nan a jerin hare haren da kungiyar Boko Haram take kaiwa.

Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane 42 a hare haren da ta kai kan wani masallaci ranar Jumma’a a Maiduguri,babban birnin jihar Borno da kuma Yola dake tazarar kilomita 400 da garin Maiduguri.

Kakakin hukumar agajin gaggawa Sani Datti yace rundunar soji tare da hadin guiwar jami’an tsaron sa kai da ake kira civilian JTF dake kokarin kakkabe kungiyar Boko haram ne suka bankadon shirin matan na kai harin ta’addanci.

Wata sanarwar da gwamnati ta fitar tace matan suna kokarin shiga unguwar Dala Ajheri ne dake garin Maiduguri lokacin da lamarin ya auku.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG