Dubun dubatan 'yan kasar Brazil sun fantsama kan titunan birane da garuruwan kasar Brazil lahadi, su na kiran da a tsige shugaba Dilma Rousseff a saboda wani abin fallasa na zarmiya, da jan kafar da tattalin arzikin kasar keyi, da kuma hauhawar farashin kayayyaki.