Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Ba Shugaban Rikon Kwarya Na APC, Victor Giadom Karfin Gwiwa


Shugaba Muhammadu Buhari.
Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya mara wa shugaban rikon kwarya na jam'iyyar APC, Victor Giadom baya.

Ya kuma bayyana cewa zai halarci taron shugabannin jam'iyyar APC da Giadom zai gudanar ta kafar yanar gizo gobe.

Mai magana da yawun shugaban Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar.

A cikin sanarwar Shehu ya umarci kafofin yada labarai da su daina yada labaran bogi a kan wannan batu.

Ana sa ran cewa gwamnoni da 'yan majalisar tarayya ma zasu halarci wannan taron na gobe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG