Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Gabatar Da Kasafin Kudin Shekarar 2017


Shugaba Mohammadu Buhari

A yau Laraba shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya gabatarwa da yan Majalisar Tarayya kasafin kudin shekara mai zuwa ta 2017.

Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin mai adadin Naira Tiriliyon 7.2, ya kuma kasafta kudin da cewa kashi 30.7 zasu tafi a manyan ayyuka irin na ma’aikatun da suka hada da: ma’aikatar tsaro da ma’aikatar Ilimi da ma’aikatar cikin gida da ma’aikatar kiwon lafiya da dai sauransu.

Ana gina kasafin kasafin kudin Najeriya bisa kudin gangar ‘danyan Man fetur a kasuwar duniya, sai kuma cin basussuka daga waje da kuma cikin gida. Cikin kudin kasafin da shugaba Buhari ya gabatar Tiriliyon 7.2, za a ciwo bashin Naira Biliyan 429 domin yin ayyuka.

Lakabin kasafin kudin bana shine ‘kasafin kudin bunkasa tattalin arziki’ wanda ke nufin kasafine da zai fitar da Najeriya daga kangin talauci da rashi da kuma farfado da tattalin arzikin kasar na din din din.

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG