Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Gana Da Sanatoci 22 Da Ke Barazanar Komawa PDP, An Yi Sasanci


Shugaba Buhari da wasu daga cikin sanatoci yayin da suka yi wata ganawa
Shugaba Buhari da wasu daga cikin sanatoci yayin da suka yi wata ganawa

“Mun yi nasara a tattaunawar da muka yi da shugaban kasa, saboda haka, yanzu batun ficewa daga jam’iyyar ya wuce.” In ji Kalu.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya gana da sanatocin jam’iyyar APC 22 da ke barazanar ficewa daga jam’iyyar.

Mai tsawatarwa a Majalisar Dattawan kasar, Sanata Orji Uzor Kalu ne ya jagoranci sanatocin zuwa fadar shugaban kasar a ranar Talata.

A cewar Kalu, jam’yyar mai mulki ta kamo bakin zaren barakar da ke sa sanatocin suke yunkurin ficewa daga APC.

Rahotanni sun ce jam’iyyar adawa ta PDP suke shirin komawa.

“Na jagoranci sanatoci 22 da ke korafi da sauran mambobin jam’iyyar APC zuwa gaban Shugaba Muhammadu Buhari.

Lokacin da Buhari yake jawabi a ziyarar da sanatoci 22 da ke barazanr komawa PDP suka kai masa (Hoto: Facebook/Fadar shugaban kasa)
Lokacin da Buhari yake jawabi a ziyarar da sanatoci 22 da ke barazanr komawa PDP suka kai masa (Hoto: Facebook/Fadar shugaban kasa)

“Mun yi nasara a tattaunawar da muka yi da shugaban kasa, saboda haka, yanzu batun ficewa daga jam’iyyar ya wuce.” In ji Kalu, wanda ya wallafa wannan sanarwa hade da hotunan sanatocin tare da Shugaba Buhari a fadarsa.

Tun bayan da aka kammala zabukan fitar da gwani a jam’iyyun siyasar Najeriya, masu takara da dama da ba su yi nasaraba, sun yi ta nuna korafi musamman a jam’iyyar APC, kan yadda aka gudanar da zabukan.

A makon da ya gabata, rahotannin sun yi nuni da cewa tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya Fani Kayode, ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar ta APC da su tashi tsaye, domin wasu sanatoci 22 na shirin ficewa daga jam’iyyar zuwa PDP.

Akalla sanatoci bakwai ne suka ficewa daga jam’iyyar ta APC ya zuwa yanzu.

Majalisar Dattawan Najeriya na da sanatoci 109, 65 daga cikinsu ‘yan jam’iyyar APC ne kafin tasowar wannan guguwar sauya sheka da ta biyo bayan zabukan fitar da gwani.

XS
SM
MD
LG