Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Kaddamar da Kwamitin Karbar Mulki


Muhammadu Buhari.

Shugaban Kasa mai jiran gado, Janar Muhammadu Buhari ya nada kwamitin 18 karkashin jagorancin Mallam Ahmed Joda domin zama wakilansa a wajen karbar tsare-tsaren mulki daga hannun gwamnati mai barin gado ta PDP.

Aikin wannan kwamiti shine yin nazari, da tacewa akan duka rahotanni masu yawan gaske da gwamnati mai barin gado ta shirya, da kuma sa ido a wadansu ayyukan shi shugaba mai jiran gado ya baiwa kwamitin.

Daya daga cikin ‘ya’yan wannan kwamiti Barrista Solomon Dalung yayiwa Sashen Hausa na Muryar Amurka karin bayani akan ayyukan da aka basu.

“Zamu yi nazari, sai kuma mu fidda bayanai bisa akan ko mene ne yake kunshe domin amfanin gwamnati mai zuwa. Sannan kuma bayan wannan, aikin ya umarce mu zana wa wannan gwamnati mai zuwa tsari da zai kasance makomanta”.

A zaben ran 28 ga watan Maris ne Jam’iyyar PDP dake rike da mulkin Najeriya na tsawon shekaru 16 ta sha kashi a hannun jam’iyyar adawa ta APC. Bugu da kari, APC ta kwace kujerun gwamnoni da na ‘yan majalisu a duk fadin Najeriya a babban zaben da aka kamala a baya-bayannan.

Wannan shine karo na farko a tarihin Najeriya da jam'iyyar dake kan mulki ta sha kashi, kuma take shirin mika mulki ga jam'iyyar adawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Shiga Kai Tsaye

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG