Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Kaddamar Da Shirin Noman Rani Na Wannan Shekarar A Jahar Kebbi


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A wata hobbasa ta bunkasa noman rani a Najeriya, gwamnatin kasar ta zabi jahar Kebbi don kaddamar da noman rani na wannan shekarar, ganin yadda jahar ta fi kowacce noma shinkafa da alkama, wadanda aka fai ci a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyarar aiki a jahar Kebbi, inda zai jaddada muhimmancin noman rani da sauran nau’ukan noma da sana’a. hasali ma ya kaddamar da noman ranin a jahar ta Kebbi, wacce ita aka zaba wannan shekarar don kaddamar da noman ranin. Baya ga haka ma Shugaba Buhari ya kaddamar da wani shiri na bayar da tallafi ga manoma.

Wannan shiri na bayar da tallafi ga manoma ya dan banbanta da wanda aka zaba gani saboda sabanin shirin baya na bai wa manya da matsakaitan manoma, wannan shiri na musamman na baiwa kananan manoma tallafi ne.

Babban Bankin Najeriya da hadin gwiwar gwamnatin tarayyar najeriya ne ke daukar nauyin wannan shirin. Wakilinmu y ace wannan ne karo na farko da aka kaddamar da shiri irin wannan, wanda gwamnati mai ci ke kokarin ganin nasararsa wajen karfafa kananan manoma. Wakilinmu y ace an zabi jahar Kebbi don kaddamar da shirin ne saboda it ace jahar da ta fi noman shinkafa da alkama, wadanda aka fai ci a Najeriya.

Ga wakilinmu na Shiyyar Sakkwato Murtala Faruk Sanyinna da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG