Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Nada Usman Alkali A Matsayin Sabon Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya


DIG Usman Alkali Baba
DIG Usman Alkali Baba

Hakan na nufin zai maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu wanda Buhari ya nada a ranar 15 ga watan Janairun 2019.

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Usman Alkali Baba (DIG) a matsayin mukaddashin Sufeton Janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Ministan hukumar kula da sha’anin ‘yan sandan kasar Maigari Dingyadi ne ya fadawa manema labarai wannan sauyi a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

Mai baiwa shugaba Buhari shawara kan al'amuran kafofin sada zumunta na zamani Bashir Ahmed, ya ruwaito Dingyadi yana cewa, "sabon nadin zai fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba."

Karin bayani akan: Usman Alkali Baba, DIG, Mohammed Abubakar Adamu, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.

Hakan na nufin zai maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu wanda Buhari ya nada a ranar 15 ga watan Janairun 2019.

Shekarun yin ritayar Adamu sun cika tun a farkon shekarar nan, amma duk da haka Buhari ya kara mai wa'adinsa, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

XS
SM
MD
LG