Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Soke Taron Majalisar Zartaswa Na Wannan Makon


Shugaba Mohammadu Buhari
Shugaba Mohammadu Buhari

Kowace ranar Laraba shugaban kasa Muhammad Buhari ke yin taro da ministocinsa amma ya soke na yau, lamarin da ya zama karo na biyu da shugaban ya soke taron tun dawowarsa daga Ingila watan jiya.

Ministan yada labaran gwamnatin Buhari Lai Muhammad ya ce saboda hutun sallah da aka tafi ma'aikata basu sami zarafin hada takardun da ake bukata ba dalili ke nan da shugaban kasa ya dage taron.

Kakakin shugaban kasa dake fadarsa ya ce tabbas za a iya yiwa dagen taron wata fassara daban, duk da yake ba sabon abu ba ne a ce an dage taron majalisar ministoci ba. Shi taron kansa, inji Malam Garba Shehu, kakakin shugaban, shugaban kasa ke kira ayi lokacin da yake bukata don a biya wa jama'a bukatunsu amma ba doka ba ce tace lallai sai an yi kowace Laraba.

A kan batun soma farfadowar tattalin arziki, Garba Shehu ya yi fatan fitowar ta dore domin a samu ci gaba.

Ga rahoton Sahabo Imam Aliyu da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:13 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG