Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Yi Wa 'Yan Najeriya Alkawarin Sauyi A Shekara Mai Zuwa


‘Yan Najeriya zasu ga sauyi daga salon mulkin gwamnatin cikin shekara ta 2017.

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yace duk wadanda suka fara gajiya da salon mulkin sa zasu ga sauyi a cikin shekara mai zuwa ta 2017, ta hanyar amfani da kudin da hukumar EFCC ta kwato daga wadanda aka samu da almundahana.

Shugaban wanda da alamu ya fahimci yadda mutane ke korafi kan tsadar rayuwa, ya nanata cewa bazai ci amanar mulki da masu zabe sama da Miliyan 15 suka daura masa ba.

Yace har yanzu ba a san iyakar kudin da aka sata zuwa kasashen waje ba, kuma kudin da aka samu aka kwato sune za a saka cikin kasafin kudi na shekara mai zuwa.

Sai dai wasu magoya bayan shugaban na ganin zai iya cimma nasara ne kawai ta hanyar shigar da ‘yan siyasa da ke kusa da al’umma cikin gwamnatinsa. Haka kuma dayawa daga cikin magoya bayan shugaban na ganin tamkar mota ta tashi ta barsu a tasha.

Domin karin bayani ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

XS
SM
MD
LG