Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Zabi Justice Ishaq Ya Wakilci Nigeria A ICC


Justice Ishaq Usman

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya zabi shugaban alkalin alkalai na birnin Abuja, Alkali Ishaq Usman a matsayin wanda zai wakilce Najeriya domin zama babban lauya a kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC).

Kotun wacce ta fara aiki ranar 1 ga watan Yulin shekarar 2002 a matsayin kotun kasa da kasa wacce ke birnin Hague na kasar Netherlands.

ICC na da ikon hukunta mutane da ake tuhuma da aikata laifukan yaki, da keta hakkin bil adama da cin zarafi da dai sauransu.

A ranar 7 zuwa 17 ga watan Disambar wannan shekarar ne ake sa ran gudanar da zaben mukamin.

Za a gudanar da zaben a hedikwatar majalisar dinkin duniya da ke birnin New York kuma za a zabi alkalai 6 wadanda zasu cika kashi daya na 3 na kotun.

Kafin yanzu, Hon. Ishaq Usman Bello ya yi aiki a kwamitoci da suka shaki shari'a daban daban.

Ya kuma yi muhimman ayyuka kamar wakiltar Najeriya a kotu da jagorantar zaman da suka shafi shari'ar zabe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG