Dazu-dazu a yau Talatan nan, shugban Najeriya yayi wata ganawa cikin sirri da wakilan gwamonin Najeriya. An yi taron ne a ofishinsa.
Tawagar gwamnonin tara, suna karkashin jagorancin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, kuma gwamnan jahar Zamfara Abdulazeez Yari.
Kamar yadda rahoton d a wakilin Sashen Hausa a Abuja Umar Farouk Musa ya aiko, gwamnonin sun gabatarwa shugaba Buhari bukatu masu yawa da suka hada da neman karin tallafin kudi domin su sauke nauyin biyan ma'aikata albashin wat da watanni da suka kasa biya.
Kakakin shugaban Najeriya Mallam Garba Shehu yace, shugaba BUhari ya gayawa gwamnonin cewa da shi a matsayin su inda suke kasa biyan ma'aikata albashi, da ko barci ba zai iya yi ba.
Ga karin bayani
Facebook Forum