Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Zai Je Daura, Duk Da Hari Kan Tawagarsa


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Hoto: Fadar shugaban kasa).
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari (Hoto: Fadar shugaban kasa).

Ga dukkkan alamu, shirin ziyarar Shugaba Buhari zuwa Daura na nan daram, duk kuwa da tauna tsakuwar da 'yan ta'adda su ka yi.

Ziyarar shugaba Buhari zuwa mahaifarsa Daura ba ta sauya ba don tawagar sharar fage ta ma’aikatan shugaban na cigaba da shirye-shiryen tarbarsa kamar yanda a ka saba.

Wannan dai ya kwantar da sharhin tunanin ba mamaki shugaban ya janye tafiyar, biyo bayan arangama da tawagar jami’ansa daga fadar Aso Rock ta yi da barayin daji kan hanyar tafiya Daura.

Rahotanni na bayyana cewa garin Daura dai na nan kamar yanda a ka saba da masu tarar shugaban kasa, wadanda su ka tsira ko tsallake rijiya da baya a kan hanyar da barayin daji ke cin karensu ba babbaka.

Daya daga cikin ‘yan jaridar fadar Aso Rock, Hassan Umar Farouk da ke Daura don dauko rahotannin ziyarar, ya ce duk tawagar na lafiya in ka debe mutum biyu da su ka samu rauni.

Hassan Farouk da ke aiki da kafar labaru ta LIBERTY ya ce shi da sauran ‘yan jarida sun shirya tsaf don zantawa da shugaban a ranar sallah.

Daura Emir's Palace
Daura Emir's Palace

Dan kamfe din shugaba Buhari da ya yi aiki a sashen shirye-shirye, Magaji Muhammad Yaya, ya ce harin wani sako ne na farkar da shugaba Buhari da gwamnatinsa yanda lamuran tsaro su ka tabarbare.

Bayan gani da ido da shugaba Buhari ya je yi gidan yarin Kuje da ‘yan bindiga su ka kai wa hari, zai zarce Dakar din Senegal don ziyarar aiki kafin daga can ya shigo Daura.

Saurari cikakken rahoton Nasiru Elhikaya:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
XS
SM
MD
LG