Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

BURUNDI: Majalisar Dinkin Duniya Zata Kira Taro


Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza.
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza.

A yau Talata ne Saudi Arabiya ta fitar da sanarwar hada sabuwar rundunar sojojin hadin guiwa ta kasashen musulmi har 34 domin yaki da ta’addanci.

An dai shirya yin taron na ranar Alhamis ne bisa bukatar yin hakan da Amurka tayi tare da goyon bayan wakilai 17 da wasu kasashe ‘yan kallo 25 a cikin hukumar. Ghana itace kasar Afirka tilo da ta goyi bayan ‘daukar wannan matakin.

Wannan shine taron musamman na farko da za’a gabatar tun watan Afrilu, da jami’an hukumar kula da kare hakkin bil Adama suka hadu don tattaunawa kan hare hare da keta yancin ‘dan Adam da kungiyar Boko Haram ke yi a Arewacin Nijeriya.

Taron na ranar Alhamis zai yi nazarin wani vdaftarin kudurin dake neman kwamishinan kare hakkin bil Adama na MDD, Zeid Ra’ad al-Hussein, ya aika da kwararru zuwa Burundi cikin kwanaki 45 domin su gudanar da bincike kan tashe tashen hankulan dake faruwa da neman hanyoyin da za’a kawo karshen su.

Tun cikin watan Afrilu ne dai Burundi take fuskantar tashe tashen hankula bayan da shugaba Pierre Nkurunziza, ya ayyana zai yi tazarce.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG