Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Canji Bai Yiwuwa Cikin Dare Daya Inji 'Yan APC


Sabon Zababben Shugaban Najeriya.

Yayin da ake ta shirye shiryen rantsar da sabon zababben shugaban kasa a Najeriya, jama’ar kasar na sa ran abubuwa da dama zasu canza musamman ganin yadda kasar ta dade cikin halin kaka nikayi.

Yayin da ake ta shirye shiryen rantsar da sabon zababben shugaban kasa a Najeriya, jama’ar kasar na sa ran abubuwa da dama zasu canza musamman ganin yadda kasar ta dade cikin halin kaka nikayi.

Mukarraban zababben shugaban na Najeriya suna cigaba da yada manufofi da kuma alkawurran da shugaban yayi ma al’umar kasar a lokacin da yake yakin neman zabe a duk fadin kasar da kuma bada tabbacin cewar gwamnatin zata cika alkawurranta.

Koda shike canji bai samuwa cikin dare daya musamman ganin shekarun da aka dade ana abubuwa da dama wadanda basu dace ba. Sanata Hadi Sidika na daya daga cikin wadanda suke cigaba da yada wannan manufa kuma yayi Karin bayanin cewa;

“Lallai sabuwar gwamnatin zatayi iya bakin kakarinta amma jama’a baza su ga canjin cikin dan kankanen lokaci ba a sakamakon irin barnar da aka dade ana tafkawa a kasar, kuma sai Janar Buhari ya zauna ya fahimci yanayin barnar kafin sanin yadda zai tafiyar da aiyukan sa. Amma daga ranar da aka rantsar da shi jama’a zasu san lallai akwai canji domin duk wanda ya karya doka za’a hukunta shi.”

Ta bangaren ‘yan PDP kuma, sun nuna cewa bazasu yi kiyayya da ‘yan jam’iyyar APC ba. Sanata Walid Jubril shine sakataren amintattun PDP, yayi Karin bayannin cewar jam’iyar su bazata mutu ba amma zasu yi adawa mai tsafta domin ciyar da kasar gaba. Kuma a cewar sa yabon gwani ya zama dole, baza su soki duk wani abu da zai kawo cigaban kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG