Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

CBN Ya Rage Harajin Tsaron Intanet Zuwa Kaso 0.005%


Babban bankin Najeriya CBN
Babban bankin Najeriya CBN

Ragin ya biyo bayan gabatar da harajin da aka yi a farkon shekarar nan me cike da cece-kuce, al’amarin daya gamu da turjiya daga kungiyoyin kwadagon NLC da TUC da kuma masu hulda da banki.

Babban Bankin Najeriya (cbn) ya rage yawan harajin bada kariya ga intanet a hada-hada ta na’ura daga kaso 0.5% zuwa kaso 0.005% cikin 100 a sabon jadawalinsa na harkokin kudin na shekarar 2024 zuwa 2025.

“CBN zai ci gaba da tursasa biyan harajin dole na kaso 0.005 cikin 100 a kan dukkanin cinikayyar da bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi suka yi ta na’ura, a cewar dokar yaki da laifuffukan intanet, ta 2015.”

Harajin, wanda aka gabatar karkashin dokar yaki da laifuffukan intanet ta 2015, wacce aka sabunta a 2024, an kirkire shi ne domin tallafawa asusun yaki da laifuffukan intanet na kasa, da ofishin mashawarcin shugaban kasa akan harkokin tsaro ke gudanar da shi

Za’a caji kaso 0.005 cikin 100 a kan dukkanin cinikayyar da bankunan kasuwanci dana hada-hada tsakanin kamfanoni da bankunan da basa mu’amala da kudin ruwa da hada-hadar kudi ta na’ura da sauransu.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG