Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea Ta Dage Taron Gabatar Da Graham Potter


Hukumar Kwallon Birtaniya
Hukumar Kwallon Birtaniya

Chelsea ta soke taron manema labarai don gabatar sabon kocin kungiyar Graham Potter, biyo bayan mutuwar Sarauniyar Ingila.

WASHINGTON, DC - Da karfe 1:30 na rana agogon yankin aka shirya yin taron manema labarai a yau Juma'a don gabatar da Potter a karon farko a matsayin kocin Blues a filin atisayen Chelsea na Cobham.

Kafin mutuwar Sarauniyar Ingila Elizabeth ta biyu ranar Alhamis aka sanar da hakan, amma daga baya Chelsea ta dauki matakin soke taron.

Wannan matakin na zuwa ne sakamakon rashin tabbas akan ko wasannin kwallon kafar Ingila na karshen mako zai gudana kamar yadda aka tsara ko a'a. An kuma sanar cewa za’a dage wasannin Premier.

Potter ya bar kungiyar Brighton, inda ya karbi kocin Chelsea biyo bayan korar Thomas Tuchel a ranar Laraba 7 ga watan Satumba, kasa da sa’o’i 24 da kungiyar ta sha kaye a hannun Dinomo Zagreb.

Yanzu haka dai an zuba ido aga ko sabon mai horar da Chelsea zai iya farfado da kungiyar daga barcin da ta ke yi.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG