Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Chelsea ta Haye Zuwa Wasan Kusa da Karshe - 8/4/14


Kugiyar kwallon kafar Chelsea, daga Ingila ta samu nasarar zuwa wasa na kusa da karshe a gasar zakarun kungiyoyin kwallon kafa na Turai, bayan lallasa wa PSG ci 2 da babu a gidan Chelsea din.

Idan ba'a manta ba, PSG ta samu nasarar zuba wa Chelsea din ci 3-1 a wasan farko da aka yishi a can Faransa Larabar da ta wuce, to yau fa Chelsea ta rama, sai dai ci biyu tayi, kuma ta hana PSG din cin kwallo ko daya. Saboda ci daya da Chelsea tayi wa PSG a gida a makon da ya wuce, kuma da yake idan aka tara kwallayen da suka jefa wa juna, an tashi 3-3 kennan, kuma Chelsea itace a gaba.

Dartmont dama ba'ayi tsamannin zata wuce zuwa wasan na kusa da karshe ba, a karawar da tayi da Real Madrid, saboda ta zuba wa Real ci 2-0, amma nasarar da Real ta samu a kanta a makon da ya wuce ya dorata akan Dartmont. Yanzu an gama da Dartmont a wannan gasa.
XS
SM
MD
LG