Kafin ta buga kwallo da Galatasaray, Chelsea ta karrama tsohon dan wasanta Didier Drogba wanda ke buga ma Galatasaray a yanzu, amma ta doke su a fili
Chelsea Ta Karrama Didier Drogba - Ta Doke Kungiyarsa ta Galatasaray - 20/3/2014
1
Magoya bayan Chelsea a bayan wani makeken kyalle na tunawa da tsohon dan wasansu Didier Drogba, lokacin da yaje a matsayin dan wasan Galatasaray domin gasar cin kofin Zakarun Kulob na Turai Talata 18 Maris, 2014
2
Wata mai gotyon bayan kungiyar Chelsea rataye da kyalle mai hoton rtsohon dan wasan Chelsea wanda ya koma Galatasaray, Didier Drogba, lokacin da kungiyoyin biyu suka kara a Stamford Bridge, Talata 18 Maris 2014
3
Didier Drogba na Galatasaray ya rungumi tsohon abokin wasansa a Chelsea, John Terry, a karshen karawar da suka yi a gasar cin kofin Zakarun Kulob na Turai a filin wasa na Stamford Bridge dake London, Talata 18 Maris, 2014
4
Didier Drogba na Galatasaray da Samuel Eto'o na Chelsea su na gaisawa da juna kafin karawar da kungiyoyin nasu biyu suka yi a Stamford Bridge Talata 18 Maris, 2014