WASHINGTON D C —
Shugaban China Xi Jinping ya gana da wasu wakilan Amurka dake tattaunawa akan batun cinikayya tsakanin kasashen biyu a Beijing yau Jumma’a, yayinda Chinar da Amurka ke kokarin cimma yarjejeniyar kasuwanci.
Sakataren ma’aikatar baitulmanin Amurka Steven Mnuchin ya rubuta a shafin sa na Twitter yau Jumma’a cewa, shi da wakilin Amurka akan batun cinikayya Robert Lighthizer sun yi wani muhimmin zama da mataimakin firayin ministan China Liu He.
Za a ci gaba da yin wani zagayen zaman shawarwarin cikin mako mai zuwa a nan birnin Washington, a cewar kafafen yada labaran China.
Wani babban mai bada shawara akan tattalin arziki a fadar White House ya bayyana kwarin Gwiwar sa akan zaman shawarwarin da ake yi tsakanin Amurka da China.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 04, 2023
Amurka Ta Kakkabo Babban Balan-Balan Na Leken Asirin China
-
Janairu 25, 2023
Mawakiya Yar Najeriya Ta Yi Tarihi A Bikin Bada Lambar Yabo Na Oscar
-
Janairu 13, 2023
Lisa Marie Presley, Diyar Mawaki Elvis Ta Rasu
-
Janairu 11, 2023
Ana Tsaftace Yankunan Da Mahaukaciyar Guguwa Ta Ratsa A California
Facebook Forum