Kasar China, inda nan ne cutar corona ta fara barkewa, ta ce jiya Asabar ba wani dan kasar da ya kamu da cutar corona, wanda wannan ne karon farko da hakan ya faru, tun bayan da ta fara bayar da rahoto kan masu kamuwa da cutar a watan Janairu.
Humar Kiwon Lafiya ta kasar China, jiya Asabar ta ce adadin sabbin kamuwa da cutar ya yi kasa daga hudu zuwa babu daga ranar Alhamis zuwa Jumma’a, wanda ya sa adadin wadanda su ka mutu sanadiyyar cutar ya kai sama da 4,600 a hukumance sannan wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar kuma kusan 83,000.
(Hotunan cutar corona)
Tsauraran matakan hana zirga zirga sun taimaka ma China wajen shawo kan yaduwar cutar a sassan kasar, wadda ta ga matukar raguwar masu kamuwa da cutar tun daga watan Maris.
Akwai masu dauke da cutar COVID-19 wajen biliyan 5.2 a duniya da kuma wanda da su ka mutu wajen 339, 000, a cewar jami’ar John’s Hopkins.
Annobar ta sa kasashe na ta fama da yadda za su kare mutane sannan kuma a lokaci guda su bude harkokin hada hadar tattalin arziki, wanda hakan ya kawo tangarda ga yadda Musulmi kan yi bukukuwa Sallah bayan watan azumi na Ramadan da kuma bukukuwan Memorial Day na tunawa da sojojin Amurka da su ka mutu yayin aikin kare muradun kasar. Wanda bisa al’ada Amurka kan je shakatawa a gabobin ruwa da gandun shakatawa.
Facebook Forum