Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Chloroquine" Na Iya Zama Makarin Coronavirus - Trump


Wasu likitoci yayin da suke kokarin gudanar da ayyukansu

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce wasu magunguna biyu suna nuna alamun za su iya zama makarin cutar coronavirus da ta addabi duniya.

Yayin wani taron manema labarai da aka yi a jiya Alhamis a Fadar White House, shugaban na Amurka ya ce maganin cutar malaria da aka fi sani da "Chloroquine" a turance, wanda aka dade ana amfani da shi, ya nuna sakamako mai kyau a binciken da ake yi.

Hakan na faruwa ne a kokarin da ake yi na gano maganin cutar ta COVID-19, yana mai cewa "ba da bata lokaci ba za a gaggauta samar da maganin na chloroquine.

A cewar Trump maganin ya jima bil adama na amfani da shi, saboda haka, babu fargabar ko zai iya kashe wani, yana mai kwatantashi a matsayin maganin da zai iya "sauya al'amura."

Baya ga maganin na Chloroquine, ana kuma ganin haske akan maganin da ake kira Remdisivir, wanda aka samar da shi domin yaki da cutar Ebola, wanda shi ma Trump ya ce, hukumar kula da magunguna da abinci ta FDA a Amurka za ta yi nazari akansa.

Sai dai ​Kwamishinan hukumar Dr. Stepehen Hahn, ya ce, akwai bukatar a gwada amfani da magungunan a dakunan bincike kafin a fara amfani da su wajen warkar da cutar ta coronavirus.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG