Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ciki Da Gaskiya - DPO a Bauchi Ya Kashe Matasa Biyu Don Sun Saci Kaji (Kashi Na Biyu) Satumba 07, 2020


Sarfilu Hashim Gumel

A makon da ya gabata ne muka fara kawo muku labarin zargin wani DPO na rundunar ‘yan sanda a cikin garin Bauchi, mai suna SP Baba Ali Mohammed, wanda ya ganawa wasu matasa uku azaba ta hanyar daure su da dukan su da tabarya, ya karya mu su sawaye da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar biyu daga matasan.

Mun dai ji yadda 'yan sandan su ka kai gawar daya daga cikin yaran mai suna Babangida Kamfala gida wajen iyayen sa don jana'iza.

A wannan makon za mu ji yadda kungiyar PIDI mai kare hakkin 'yan adam ta daura aniyar bin kadun wadannan matasa don tabbatar ganin an yi musu adalci.

Tuni mutane a Bauchi sun fara kira ga babban sufeton 'yan sandan Najeriya Muhammad Adamu da sauran mahukunta su da su dauki matakin hunkuta SP Baba Ali Mohammed ko kuma a gurfanar da shi gaban kotu, don yiwuwar fuskantar mafi tsananin hukunci bisa laifin kisa da a ke zargin ya aikata.

A yi sauraro lafiya.

Ciki Da Gaskiya - DPO a Bauchi Ya Kashe Matasa Biyu Don Sun Saci Kaji (Kashi Na Biyu) - 11'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:11:00 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG