Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ciki Da Gaskiya - Takaddamar Fili Tsakanin Sarki da Talakansa, Kashi na Daya - Oktoba 18, 2021


Sarfilu Hashiim Gumel

A sabon shirin mun leka garin Miya a jihar Bauchi, inda wani bawan Allah mai suna Alhaji Bala Idris ya zargi Sarkin garin da neman amfani da karfin sarauta wajen kwace ma sa filin sa da ya ce ya samu daga gwamnati.

Wannan dambarwa ta shafi Sarkin Miya da dan sa, wadanda Alhaji Bala ke cewa su na son su nuna ma sa sun fi karfin doka.

A na sa bangaren Sarkin na Miya Sulaiman Yakubu ya ce wannan batu ba gaskiya bane, kumaakwai alamar talauci na damun Alhaji Bala wanda har ya sa shi wannan zargi.

Sarkin na Miya ya kara da cewa akwai lokacin da ya baiwa Alhaji Bala wani fili kyauta amma yace shi baya so.

A yi sauraro lafiya:

Ciki Da Gaskiya - Takaddamar Fili Tsakanin Sarki Da Talakansa, Kashi na Daya - 10'37"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:37 0:00


XS
SM
MD
LG