Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikin Kwanaki Dari Buhari Ya Karya Karfin Boko Haram


Boko Haram

A firar da yayi da Muryar Amurka Sanata Ali Ndime mai wakiltar kudancin Borno yankin da kungiyar Boko Haram ta fi daidaitawa ya bayyana irin nasarorin da shugaba Buhari ya samu cikin kwanaki dari akan mulki.

A kan batun tsaro Sanata Ndime yace jama'a da duniya suna gani akwai cigaba da aka samu.

Yanzu akwai hadin kai na kasashe wanda a da babu shi. A manyan kasashen duniya da aka dangana dasu su bada tallafi yanzu sun farga daga zuwan shugaba Buhari. Duniya ta samu karfin gwiwa na niyar taimakawa.

Ana samun nasara. Misali muanen Gwozah sun fara matsawa suna son su koma gidajensu da suka baro. Yanazu ana tanadin yadda za'a mayar dasu.

Kamar yadda shugaban kasa ya fada kafin karshen wannan shekarar za'a gama da kungiyar Boko Haram.

Makon jiya sama da mutane dubu sun bar Maiduguri sun koma yankunansu. Gwamnan jihar Borno ya taimaka da motoci kana sojoji suka yi masu rakiya.

A Gwozah an fara cin kasuwa. Masllatai na gudanar da sallar Juma'a haka kuma mijami'u na sujada ranar Lahadi.

Dangane da hare-haren da har yanzu 'yan kungiyar suna kaiwa Sanata Ndime yace ba zasu dauke rana daya ba. Yanzu babu tashin bam kamar da.Yanzu ma harin da suke yi na neman abinci ne.

Yanzu 'yan Boko Haram basu da bindigogi irin na zamani. Da adaka suke kai hari saboda duk hanyoyin samun makamai an toshe. Hanyoyin samun kudi da zasu sayi makamai babu kuma. Basu da motoci ko man fetur dalili ke nan yanzu suna kai hari kan dawaki.

Ko shakka babu karfin kungiyar Boko Haram ya ragu sosai. A kan 'yan matan Chibok kuma Sanata Ndime yace yanzu da shugabancin Buhari suna da karfin gwiwar zasu dawo.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:31 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG