Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cikin Mutanen Da Mahukumtan Iran Suka Tsare Daya Ya Mutu


Masu zanga zanga suna dauke da hoton kan shugaban koli na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei

Yan Iran sun kwashe mako daya suna zanga zangar rashin amincewa da manufar gwamnatin kasar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 22 tare da cafke wasu 1,000 da aka ce su ne shugabannin masu boren

Yayinda yake jawabi, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya ce masu zanga zanga na da wasu dalilan da suka harzukasu baicin na kuncin tattalin arziki kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito

Inji Hassan Rouhani matsalar harkokin siyasa da na zaman yau da kullum a kasar na cikin dalilan da suka harzuka mutanen, musamman matasa, shiga boren. Ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta sassauta yin anfani da kafafen sada zumunta irinsu Facebook da Twitter domin ba mutane sukunin fadin albarkacin bakinsu da cudanya da juna.

To saidai Hamid Shahriari mataimakin shugaban hukumar shari’a ta kasar ya ce za’a gurfanar da wadanda aka kama gaban shari’a domin a hukumtasu. A cewarsa wasunsu na iya fuskantar hukumcin kisa.

A wani gefen kuma Tayebeh Siavashi dan majalisar dokokin kasar, yace kamfanin labaran kasar, ILNA ya tabbatar masa da mutuwar wani matashi mai shekara 22 da haihuwa da aka kama lokacin zanga zangar. Matashin da ya mutu a kurkukun wai ya kashe kansa ne.

Yawancin masu zanga zangar, kamar yadda kamfanin Reuters ya ruwaito, suna zargin manufar kasar ta Iran a Gabas ta Tsakiya kamar yadda ta yi katsalandan a kasashen Syria da Iraq. Makudan kudin da kasar ke kashewa akan Falesdinawa da kungiyar Hezbollah ta Lebanon maimakon gwamnatinsu ta taimaka da habaka tattalin arzikin kasar da zai taimakesu ya kara tunzura masu boren (Reuters)

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG