Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ciwon Bugun Zuciya Ya Kai Babanmu Maitama Jinya A Al-Qahira


Alhaji Yusuf Maitama Sule, Dan Masanin Kano,

Babban dan marigayin, Alhaji Mukhtari Maitama, ya fadawa VOA Hausa cewa a ranar Asabar da ta gabata ne Alhaji Yusuf Maitama Sule ya bar Najeriya zuwa al-Qahira a kasar Misra don jinya.

Alhaji Maitama Sule ya rasu ya bar 'ya'ya goma, maza hudu da mata shida ya kuma bar mata daya.

Lokacin da ya kai kasar Misra sun yi wasu gwaje gwaje inda suka gano wasu lallurorin amma kafin ma su yi masa wani abu rai yayi halinsa yau da safe.

Maitama Sule mutum ne mai juriya da hakuri. Yana kuma girmama kowa. Ya nuna wa 'ya'yansa kada su raina kowa ko tsangwamar kowa. Yadda yake karbar mutane haka yake cudanya da 'ya'yansa.

Allah Ya ba shi baiwar iya magana kuma kowa na son ya saurare shi. Amma duk da haka bai yadda 'ya'yansa su yi girman kai ba dominsa. Ko alfarma baya neman wa 'ya'yansa daga gwamnati. Amma su 'ya'yan idan sun kwankwasa kofar gwamnati da sunansa a kan sauraresu. Ya koya wa 'ya'yansa su nemi abu da kanusu.

Za'a yi janaizarsa gobe Talata da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:07:35 0:00

Facebook Forum

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG