Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta ce mutuwar Fazul Abdullah Mohammed, wanda ake zargi da jagorantar harin da aka kai a Ofishin Jakadancin Amurka a gabashin Afirka a 1998, ta sa al-Ka’ida sake samin cikas.
Hukumomi a Somaliya sun fadi ran Asabar cewa an kashe jigon na al-Ka’ida kwanaki biyar da su ka gabata a wani wurin duba ababen hawa da ke cikin birnin Mogadishu.
Misis Clinton, wadda ke ziyarar aiki a Tanzania, t ace mutuwar Fazul itace babbar asara ta biyu da al-Ka’ida ta yi tun bayan da dakarun Amurka na musamman suka kashe Osama bin Laden a watan jiya.
Kungiyar ta al-Ka’ida ta kai hari kan Ofisoshin jakadancin Amurka a Nairobin Kenya da Dar es Salam din Tanzania ran 7 ga watan Agustan 1998, suka hallaka mutane 224.
Ran Lahadi, Sakatariya Clinton ta age fulawa a wurin tuna ‘yan Tanzaniya 12 din da aka kashe a harin bom din Dar es Salam.