Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Copa del Rey: Wasan Karshe Tsakanin Real Madrid Da Osasuna

Wasan karshe na Copa del Rey
Wasan karshe na Copa del Rey

Sau 19 Madrid tana lashe kofin na Copa del Rey, karo na karshe a shekarar 2014.

Real Madrid za ta kara a wasan karshe da Osasuna a filin wasa na La Cartuja a kokarin lashe kofin Copa del Rey.

Wasan na karshe zai wakana ne yayin da Madrid ke taga-taga a gasar La Liga.

Wannan shi ne karon farko da Osasuna take harin lashe wani babban kofi.

Sau 19 Madrid tana lashe kofin na Copa del Rey, karo na karshe a shekarar 2014.

A Italiya kuwa, AC Milan da Inter Milan na shirin fuskantar manyan wasanni.

Milan za ta kara da Lazio a San Siro yayin da Inter za ta kai ziyara gidan Roma.

Sakamakon wadannan wasanni na Italiya shi zai fayyace wadanne kungiyoyi ne za su kara a gasar Zakarun Nahiyar Turai.

XS
SM
MD
LG