Lura da dumbin 'yan kasar China da ke zaune a birnin Damagaram na Jamhuriyar Nijar wadanda kan yi zirga-zirga daga kasaru zuwa kasar ta Nijar, hukumomin yankin sun fara daukan matakan bullar cutar Coronavirus da ke kisa.
Akwai 'yan kasar China ba adadi masu aiki a wurare kamar a babban asibitin yankin, da kamfanin matatar man fetur na SORAZ, zuwa 'yan kasuwa a Damagaram da kan yi zirga-zirga tsakanin yankin da China.
Cutar dai kamar yadda likitoci suka yi bayani, tana saurin yaduwa, hakan ne ya sanya jagororin kamfanin SORAZ suka daukan matakan kariya.
Jami'in kula da huldar jama'a a kamfanin, Ellemi Bukar, ya ce ba fita, ba shiga - wato wandanda suka je China kar su koma Damagaram, hakan nan wandanda suke SORAZ kar su je China.
Ita ma hukumar kiwon lafiya ta jihar Damagaram ta yi nata yunkuri wajen daukan matakan, inda yanzu haka a cewar mataimakiyar Darekta, Madame Hadi Fatsuma Inki, suna wata ganawa da wakilan hukumomin kiwon lafiya na Duniya irin su OMS, da ta Afirka OAS, Croix Rouge da sauran su.
Sai dai baya ga cutar ta Coronavirus, mazauna Damagaram da kewaye da ma sauran 'yan kasar sun nuna fargaba da damuwa kan bullar cutar Lassa Fever a Najeriya da ke makwabtaka da Nijar.
Ko da yake, hukumomi sun ce nan gaba za su yi karin bayani game da wannan cuta.
Saurari rahoto cikin sauti daga wakiliyar Muryar Amurka Tamar Abari.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 01, 2023
Kamaru Ta Cire Tallafin Man Fetur
Facebook Forum