Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Adadin Najeriya Ya Kai 305


Wasu ma'aikan lafiya suna feshi saboda cutar coronavirus a Korea ta Kudu

Hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC a Najeriya, ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar ya kai 305.

Adadin ya kai wannan mataki ne bayan da aka samu karin mutum 17 da ke dauke da cutar a sassan kasar.

“A ranar 10 ga watan Afrilu, an samu sabbin masu dauke da cutar COVID-19 17 a Najeriya.” NCDC ta bayyana a shafinta na yanar gizo.

“Ya zuwa yanzu, ana da tabbacin mutum 305 ke dauke da cutar, an sallami mutum 58 kana bakwai sun mutu.”

Cikin mutum 17 da aka gano, 8 a Legas suke, uku a Katsina, biyu a Abuja, daya a Niger, daya a Kaduna, daya Anambra sannan daya kuma a Ondo,” kamar yadda shafin na NCDC ya nuna.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG