Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: An Samu Karin Mutane 313 A Najeriya


A cikin sababbin alkaluman da hukumar dakile cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar, wasu daruruwan mutane sun sake kamuwa da cutar coronavirus.

A cewar NCDC, mutum 313 ne cutar ta sake harba, wanda hakan ya mayar da adadin masu cutar zuwa 7,839 a kasar.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar, inda yanzu ta sake samun sabin mutum 148. Sai birnin tarayya Abuja da karin mutane 36.

Sauran jihohin sun hada Rivers 19, Edo 13, Kano 13, Ogun 12, Ebonyi 11, Oyo 7, Plateau 6, Kaduna 5, Kwara 4, Akwa Ibom 3, Bayelsa 3, Niger 2, sai jihar Anambra dake da guda daya.

A cewar hukumar, a yanzu haka Najeriya na da mutane 7,839 wadanda suka kamu da cutar, yayin da mutane 2,263 suka samu lafiya, sai kuma mutane 226 da suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG