Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: An Samu Karin Mutane 416 Da Suka Kamu Da Cutar a Najeriya


A cikin sababbin alkaluman da hukumar dakile cututtuka ta Najeriya, NCDC ta fitar, wasu daruruwan mutane sun sake kamuwa da cutar coronavirus.

A cewar NCDC, mutum 416 ne cutar ta sake harba, wanda hakan ya mayar da adadin masu cutar zuwa 10,578 a kasar.

Har yanzu dai jihar Legas ce ke kan gaba wajen yawan masu dauke da cutar, inda yanzu ta sake samun sabbin kamuwa 192.

Sauran jihohin sun hada Edo (41), Rivers (33), Kaduna (30), Kwara (23), Nasarawa (18),Borno (17), Birnin tarayya Abuja (14), Oyo (10), Katsina (7), Abia (5), Delta (5), Adamawa (4), Kano (4), Imo (3), Ondo (3), Benue (2), Bauchi (2), Ogun (2), Nijer (1).

A cewar hukumar, a yanzu haka Najeriya na da mutane 10,578 wadanda suka kamu da cutar, yayin da mutane 3,122 suka samu lafiya, sai kuma mutane 299 da suka mutu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG