Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Gwamnatin Jihar Filato Na shirin Gudanar Da Aikin Feshi


Gwamna Simon Lalong

Gwamnatin jihar Filato ta umurci daukacin mazauna jihar da su kasance a cikin gidajensu har tsawon mako guda don bata damar yin feshin maganin kashe kwayoyin cututtuka, wannan na zaman wani mataki na dakile yaduwar cutar COVID-19 da ta addabi kasashen duniya.

Gwamnan jihar, Simon Lalong, ya ce daga karfe sha biyun dare na ranar Alhamis 9 ga watan Afrilu zuwa ranar Laraba 15 ga watan Afrilu za a gudanar da aikin feshin.

Hukumomin jihar zasu yi kokarin tabbatar da cewa babu wanda ya fita daga gidansa, sai wadanda ke gudanar da ayyuka na musamman kamar jami'an tsaro, ma'aikatan kwana-kwana, jami'an kiwon lafiya, 'yan jarida, da sauransu.

Shugaban kungiyar masu motocin sufuri a jihar Filato, Alhaji Yusha’u Muhammad ya ce zasu tabbatar da an aiwatar da dokar hana zirga zirga a jihar don a iya cimma nasarar dakile wannan cuta.

Saurari karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00


Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG